Super Cup: Real Madrid za ta kara da Barcelona

Super Cup: Real Madrid za ta kara da Barcelona

- Akwai babban wasa inda Zakarun Sifen za su goge raini

- Kungiyar Real Madrid za ta buga da Barcelona an jima

- Wanda yayi nasara zai samu lashe kofin 'Super Cup'

Zakarun Sifen ne za su goge raini a wannan makon inda Kungiyar Real Madrid za ta buga da Barcelona an jima.

Super Cup: Real Madrid za ta kara da Barcelona
Real za ta buga da Barcelona

Duk wanda yayi nasara a wasanni biyun da za a buga zai dauki Super Cup na kasar Sifen wanda aka gwabzawa tsakanin wanda ya ci Gasar La-liga da kuma wanda ya ci Gasar Copa Del-Rey a kakan wasan da ya wuce.

KU KARANTA: Real Madrid za ta gwabza da United

Super Cup: Real Madrid za ta kara da Barcelona
Real Madrid ta doke Man Utd

Bayan yau, za a kara doka wasan karo na biyu a tsakiyar mako mai zuwa wanda daga nan za a gane zakara. Ana sa rai wannan karo Dan wasa Ronaldo ya dawo bakin aiki bayan ya zauna a benci a wasan su da Manchester United.

Ku na da labari cewa Kungiyar Real Madrid ta lashe Gasar UEFA Cup na Zakarun Nahiyar Turai. Kungiyar Real Madrid ta doke Manchester United da ci 2-1a wasan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Da kudi da iyali wane za ka zaba?

Asali: Legit.ng

Online view pixel