Dalilai da suke nuna bukatuwar shan lemun tsami a kowace safiya

Dalilai da suke nuna bukatuwar shan lemun tsami a kowace safiya

Hanyoyin amfani da ruwan lemun tsami ya ke inganta kiwon lafiyar dan Adam

Ga masu neman hanya mafi sauki don inganta rayuwar su da kuma lafiyar su fiye da komai. Shan ruwan lemun tsami a farkon kowace safiya abu ne mai sauki da mutum zai rinka yi kuma zai yi tasiri wajen lafiya managarciya.

Da yawan mutane da suka dauki wannan al'ada shekaru kadan da su ka gabata, sun bayyana irin tasirin da suka samu wajen inganta lafiyar su.

Bisa ga falsafar Ayurvedic, zabin kiwon lafiya da kake yi game da aiki na yau da kullum ko dai ya karfafa juriya ga cututtuka ne ko kuma ya yada ta.

Lemun tsami yana kunshe da sunadaran vitamin C, B, calcium, iron, magnesium, potassium, enzymes, antioxidants, da fibers.

Ga fa'idojin shan ruwan lemun tsami a jikin dan Adam kamar haka:

Inganta narkewar abinci cikin gaggawa

Tsarin ruwan lemun tsami yana kamanceceniya da ruwan cikin mutum saboda haka yana taimakawa wajen narkar da duk wani nau'in dafi ko guba ta abinci dake tashshin ciki na abinci. Ruwan lemun tsami yana taimakawa wajen narkewar abinci cikin sauki, kwarnafi da tashin zuciya, sannan yana sanya bayan gida mai laushi ba tare da wahala ba.

Dalilai da suke nuna bukatuwar shan lemon tsami a kowace safiya
Dalilai da suke nuna bukatuwar shan lemon tsami a kowace safiya

Inganta yakar cututtuka

Ruwan lemun tsami ya na da sunadarin vitamin c, wanda ya ke karfafa garkuwar mai yakar cututtuka ta jikin dan Adam, sannan kuma akwai sunadarin iron wanda ya ke taimakawa wajen tato duk wani sunadarin iron na cikin abinci.

Samar da wadataccen ruwa a jiki

Jikin mutum yana da matukar bukatar ruwa a kowane lokaci, saboda haka jikin mutum ya zama cikin yalwar ruwa abu ne mai fa'ida kwarai dagaske. Shan ruwan lemun tsami a kowace safiya zai taimakawa jikin dan Adam zama cikin wadataccen ruwa domin kuwa sai da ruwa kowane sashe na jikin zai yi aikin da ake bukata.

Bayar da karfin jiki

Shan ruwan lemun tsami yana sanya karfi a jikin dan Adam tun daga lokacin da aka sha shi.

Gyaran fata

Lemun tsami yana da sunadaran antioxidants da suke bayar da kariyar wajen yamushewar fata. Wanna sunadaran su na taimakawa wajen hana tsufan fata ta tamushewa, ta yadda hausa kan ce'mayar da tsohuwa ya yariya'.

KU KARANTA KUMA: Amfanin ruwan kokwamba guda 5 a jikin dan Adam

Hana ko rage kumburi

Ruwan lemun tsami su na da ikon cire sunadaran uric acid daga gabbai saboda shi uric acid shine mai assasa kumburi a jikin dan Adam.

Taimako wajen rage nauyin jiki

Lemun tsami shi kadai baya rage nauyin jiki, amma yana taimakawa wajen hana saurin jin yunwa domin yawan cin abinci yana assasa jikin mutum ya yi nauyi.

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel