Dalilin da yasa bana fitowa a fina-finan Nollywood - Nafisa Abdullahi

Dalilin da yasa bana fitowa a fina-finan Nollywood - Nafisa Abdullahi

Fitacciyar Jarumar nan da ta shahara a harkar shirya Fina-Finai na Kannywood Nafisa Abdillahi ta bayyana dalilin da yasa bata fitowa a yanzu a cikin fina-finan Nollywood inda ta bayyana cewa tayi hakan ne domin ta kare mutuncin ta.

Jarumar ta kasance basa zama a inuwa daya da Korarriyar Rahama Sadau sakamakon wani sabani daya ratsa tsakaninsu.

Ko a watannanin baya ma jaruman biyu sunyi musayar kalamai masu zafi yayinda a halin yanzu jaruma Rahama Sadau tana daya daga cikin yan wasan Nollywood wadanda tauraruwarsu ke haskawa.

A baya Legit.ng ta kawo maku inda Nafisa Abdullahi ta fito fili ta yi kasa-kasa da matan da ke anfanin da man nan mai kara fari na shafawa wato bilicin.

Dalilin da yasa bana fitowa a fina-finan Nollywood - Nafisa Abdullahi
Dalilin da yasa bana fitowa a fina-finan Nollywood - Nafisa Abdullahi

KU KARANTA KUMA: Majalisar dokoki na ma shugaba Buhari adduán dawowa lafiya – Shehu Sani

Jarumar ta yi wannan kakkausar suka ce a shafin ta na sada zumunta na Instagram inda tace hakan bai kamaci yar musulmai ba don kawai ta burge maza.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a email dinmu na labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel