Gobarar Titi a Jos: Ɗan jaridar da aka rotsa ma kai a Kaduna ya samu gwaggwaɓar kyauta daga Shehu Sani

Gobarar Titi a Jos: Ɗan jaridar da aka rotsa ma kai a Kaduna ya samu gwaggwaɓar kyauta daga Shehu Sani

Shugaban kwamitin basussukan kasashen waje, kuma sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani yayi ma wani dan jarida dake jihar Kaduna sha tara ta arziki a ranar Litinin 7 ga watan Yuli.

Shehu Sani ya aika da kyautar mota ne ga dna jaridar wanda ya sha duka a hannun wasu yan baranda da suka afka ma taron manema labaru da tsagin APC na su Sanata Shehu Sani suka shirya a ranar Lahadin data gabata, inda har aka fasa ma mutumin kai.

KU KARANTA: An kai ma Musulmai hari yayin da suke Sallah a masallaci (Hoto)

Wannan dan jarida mai suna Lawal Ahmad wanda ya fito daga gidan rediyon Liberty ya karbi wannan kyauta ne daga hannun mashawarcin Shehu Sani kan al’amuran siyasa, Suleiman Ahmad a harabar kungiyar yan jaridu a jihar Kaduna.

Gobarar Titi a Jos: Ɗan jaridar da aka rotsa ma kai a Kaduna ya samu gwaggwaɓar kyauta daga Shehu Sani
Dan jaridan

Majiyar Legit.ng ta ruwaito, shugaban kungiyar, Kwamared Adamu Yusuf ya yana ma Sanatan tare da jinjina a gare shi sakamakon irin gudunmuwar da yace yake yi ma yan jaridu, sa’annan yayi addu’ar Allah ya kiyaye na gaba.

Sai dai ba Lawal Ahmad bane kadai ya samu wannan kyauta, har da wani dan jarida na kamfanin jaridar Vanguard mai suna Luka Biniyat wanda a yanzu haka yake tsare bayan buga wani labara da yayi akan gwamnatin jihar, inji rahoton Rariya.

Gobarar Titi a Jos: Ɗan jaridar da aka rotsa ma kai a Kaduna ya samu gwaggwaɓar kyauta daga Shehu Sani
Motocin

Sai dai wannan rahoto da Biniyat ya buga bai yi ma gwamnatin jihar Kaduna dadi ba, wanda hakan yasa ta duaki gabarar ganin an hukunta shi, inda ta kai kararsa gaban kotu, zuwa yanzu dai ana gudanar da shari’arsa.

Gobarar Titi a Jos: Ɗan jaridar da aka rotsa ma kai a Kaduna ya samu gwaggwaɓar kyauta daga Shehu Sani
Lawal Ahmad

Gobarar Titi a Jos: Ɗan jaridar da aka rotsa ma kai a Kaduna ya samu gwaggwaɓar kyauta daga Shehu Sani
Shugaban kungiyar yana amsan makullin motar

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Yadda wani matashi ke samun miloyyi daga sana'ar Panke,kalla:

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel