Shin ka san irin amfanin filanten a jikin mutum

Shin ka san irin amfanin filanten a jikin mutum

- Bincike ya nuna cewa filanten da amfani kwarai da gaske

- Filanten na dauka da bitamin da sauran sinadarai iri-iri

- Filanten na maganin hawan jini da kuma rage nauyi

Shin ka san irin amfanin filanten a jikin mutum
Itacen Filanten a Najeriya

1. Hawan jini

Yawan cin filanten na sa jinin mutum ya tsaya daidai ba tare da hawa sama ko sauka kasa ba saboda irin sinadarai na fotash

2. Nauyi

Filanten na kokari wajen tsagaita nauyin mutum ya zama bai zama rusheshe ba. Filanten na kula da yawan sukarin da ke jikin mutum

Shin ka san irin amfanin filanten a jikin mutum
Soyayyen filanten na da amfani

3. Maganin cutar sukari

Haka kuma filanten na yakar cutar nan na sukari watau dayabatis. Sinadarin magnesium na kula da yanayin sikarin da ke jikin mutum.

4. Gyara kwakwalwa

Masana sun ce filanten na dauke da kaso da dama na Bitamin B6 wanda ke gyara kwakwalwa wasai. Filanten na kuma rage ciwon kai.

5. Kwarin kashi

Filanten na dauke da Sinadarin kashium da ke kara kwarin kashi da jijiyoyi da na na hakori da akaifu.

Mun tsakuro wannan daga Jaridar Thecablestyle

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani matashi yayi kudi da tallar fanke

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: