'Yan wasa 4 da za su iya gadon wajen Neymar a Barcelona

'Yan wasa 4 da za su iya gadon wajen Neymar a Barcelona

- A kakar bana Tauraron Dan wasa Neymar ya bar Barcelona

- Barcelona na neman wanda zai maye gurbin Dan wasan

- Daga ciki akwai Irin su Philip Coutinho, Dembele, da Mpape

A kakar bana Dan wasa Neymar Jr. ya sauya sheka zuwa PSG daga Barcelona kan kudi fam Miliyan €222. Ana sa rai Barcelona za ta maye gurbin sa.

'Yan wasa 4 da za su iya gadon wajen Neymar a Barcelona
Dan wasa Neymar ya bar Barcelona

1. Philip Coutinho

Barcelona na neman Dan wasan Liverpool Philip Coutinho wanda yayi kwallo tare da Luis Suarez. Kungiyar ta shirya kashe kudi kan wannan Dan wasa duk da Kocin Liverpool Jurgen Klopp bai da niyyar saida Dan wasan.

'Yan wasa 4 da za su iya gadon wajen Neymar a Barcelona
Dan wasan Liverpool Coutinho a wasan su da Arsenal

2. Ousman Dembele

Ana kawo Dan wasa Dembele cikin wadanda za su maye gurbin Neymar Jr. Shi ma dai wannan yaro akwai kwallo a Kafar sa.

'Yan wasa 4 da za su iya gadon wajen Neymar a Barcelona
Dan wasa Ousman Dembele na Dortmund

3. Kylian Mbappe

Dan wasan Monaco Mbappe yana cikin yaran da ke tashe a Duniya sai dai zai yi matukar tsada. Barcelona za ta gamu da cikas daga Real Madrid wanda ke neman Dan wasan.

'Yan wasa 4 da za su iya gadon wajen Neymar a Barcelona
Matashin Dan wasan Monaco Mbappe

4. Eden Hazard

Dan wasan Chelsea Eden Hazard yana daga cikin kwararrun 'Yan wasan Ingila da Duniya sai dai Kocin sa Conte yace bai ga dalilin rabuwa da Dan wasan sa ba.

'Yan wasa 4 da za su iya gadon wajen Neymar a Barcelona
Dan wasa Hazard zai koma wajen Neymar a Barcelona?

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wa su ka fi dacewa da albashi mafi tsoka?

Asali: Legit.ng

Online view pixel