Dandalin Kannywood: Da sana'ar fin nike ci da kai na da kuma iyaye na - Hafsat Idris

Dandalin Kannywood: Da sana'ar fin nike ci da kai na da kuma iyaye na - Hafsat Idris

Shahararriyyar jarumar nan ta wasan fina-finan Hausa na Kannywood watau Hafsat Idris ta bayyana sana'ar fim a matsayin muhimmiyar sana'ar da ta ke rufa mata asiri tare da iyayen ta.

Jarumar ta yi wannan ikirarin ne a cikin wata fira da tayi da wakilin majiyar mu lokacin da take ansa tambayoyi daga gare shi.

Dandalin Kannywood: Da sana'ar fin nike ci da kai na da kuma iyaye na - Hafsat Idris
Dandalin Kannywood: Da sana'ar fin nike ci da kai na da kuma iyaye na - Hafsat Idris

Legit.ng ta samu labarin cewa jarumar dai ta fara fim ne a watan Disambar shekarar bara ta 2016 sannan kuma dalilin yin fim din nan nata na Barauniya ya sa masu hada fina-finai na yin ruguguwar sanya ta a fina-finansu saboda yadda ta kware a lokaci guda.

Haka ma dai jarumar ta bayyana cewa kowanne wata takan yin fina-finai akalla 3 zuwa 4 saboda amincewar da furodusoshi suka yi mata wajen taka rawa a manyan fina-finai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng