Dalilin da ya sa na fito a Barauniya – Hafsa Idris
Shahararriyar Jarumar fina-finan Kannywood, ace ta shigo harkar fim da kafar dama, Hafsa Idris, ta ce ta dauki tsawon watanni shidda bitar rubutaccen labarin fim din “Barauniya” shi ya sa ta taka rawar gani sosai a fim din kamar yadda gogaggun barayi ke yi.
Hafsa, wacce ake wa lakabi da ‘Barauniya’ ta bayyana cewa ta soma fim ne domin ba ta son zaman banza. A cewarta harkar fim ya fi aikin gwamnati saboda tana samun abunda ma’aikacin gwamnati baya samu.
Sannan kuma jarumar ta bayyana cewa da harkar fim ne take hidimomin gabanta daman a iyayenta da yan’uwa.
Jarumar ta ce ta koyi darasi da dama daga fim din “Barauniya” wanda shi ne na farko da ta fara yi a kamfanin shirya fina-finai na Kannywood.
Jarumar, wadda ta soma fim a watan Disambar 2016, dalilin yin fim din Barauniya ya sa masu hada fina-finai na yin ruguguwar sanya ta a fina-finansu saboda yadda ta kware a lokaci guda.
KU KARANTA KUMA: Jirgin Shugaban kasa Buhari na nan inda aka ajiye shi har gobeJirgin Shugaban kasa Buhari na nan inda aka ajiye shi har gobe
Ta ce ko wani wata tana yin fim uku zuwa hudu saboda “amincewar da furodusoshi” suka yi mata wajen taka rawar gani a manyan fina-finai.
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng