Rashin isashen barci na janyo kiba - masana kiwon lafiya

Rashin isashen barci na janyo kiba - masana kiwon lafiya

- Binciken masana kiwon lafiya ya bayyana cewa rashin samun isashen barci yana haifar da kiba

- Binciken ya nuna cewa ma su kiba sun fi saurin kamuwa da ciwon sikari

A wani sabon binciken masana kiwon lafiya na kasar Birtaniya ya bayyana cewa rashin isashen barci ya na haifar da kiba wadda take alakantuwa da rashin ingataccen lafiyar garkuwar jiki.

Binciken wanda a ka gudanar a cibiyar bincike da makarantar binciken sinadarai na abinci da ke Birnin Leeds a kan mutane 1615 masu shekaru tsakanin 19 zuwa 65.

Ma su binciken sun debi jinin wannan mutane, nauyin jiki, fadin kugu, awon jini, irin cimar su da lokutan da kowanensu ke dauka wajen yin barci.

Rashin isashen barci na janyo kiba - masana kiwon lafiya
Rashin isashen barci na janyo kiba - masana kiwon lafiya

Sakamakon binciken ya nuna cewa ma su daukar awanni shida wajen yin barci su na da fadin kugu doriya da inci uku a kan ma su daukan awanni tara su na barci.

KU KARANTA: Yadda a ke zaman doya da manja tsakanin ma su motoci da 'yan a-daidaita-sahu a jihar Kano

A wannan binciken ne a ka gudanar a ka gano cewar ma su rashin samun isashen barci su na tare da hatsarin kamuwa da cutar ciwon sikari da rashin ingatattun sinadarai ma su kare garkuwar jiki.

Wani daga cikin ma su binciken, Greg Potter, ya bayyana cewa yawan mutane ma su kiba ya lunku har sau biyu tun daga shekarar 1980 wadda ma fi yawansu su na dauke da cuta ciwon sikari.

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng