Za mu bunkasa harkokin Musulunci a Jigawa – Gwamna Badaru
Rahotanni sun kawo cewa gwamnan jihar Jigawa, Badaru Abubakar ya jaddada kokarin gwamnatinsa na nabbaka harkokin addinin musulunci a jihar.
Gwamna Badaru ya sanar da hakan ne gurin taron kaddamar da kudaden tallafi da zaa tara saboda gina sakateriyar Izala a garin Dutse.
Ya kuma yi godiya ga kungiyar Izala da ta zabi jihar domin gudanar da taron ta na shekara- shekara, inda ya ce wa’azin da take yi na matukar inganta rayuwar alúmman jihar.
Da yake jawabi, shugaban kungiyar Izala na kasa, Sheik Bala Lau, ya nuna jihar Jigawa a matsayin jiha mai zaman lafiya, inda ya danganta hakan ga irin kyakkyawan mulkin gwamna Badaru.
An tara kudade sama da Naira miliyan 19 a wajen taron. Shugaban taron, Alhaji Isa Gerawa ya ba da tallafin Naira miliyan 5, Alhaji Haruna Mai Fata Kwalam naira miliyan 2, kananan hukumomi 27 sun ba da naira miliyan 2.5, sanata Sabo Muhammad Nakudu da majalisar jihar Jigawa sun ba da naira miliyan daya daya.
KU KARANTA KUMA: Buhari ya matsu ya dawo gida – Gwamna Ortom ya yi Magana bayan ziyarar Landan
Sai sanata Ubali Shitu da ya ba da tallafin kudade da kayan aiki na naira miliyan 3.3, ofisoshin sakatarorin gwamnati sun ba da naira dubu 650, na mashawarta sun ba da naira dubu 630, jam’iyyar Apc reshen Jigawa ta ba da naira dubu 100, da dai sauran su.
https://twitter.com/naijcomhausa
https://www.facebook.com/pg/naijcomhausa/posts/?ref=page_internal#
Don bamu shawara ku aiko mana da labarai, tuntubemu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng