Cutar yoyon fitsaro: Ministan Lafiya yayi ma marasa lafiya tiyata a asibiti da kansa (Hoto)

Cutar yoyon fitsaro: Ministan Lafiya yayi ma marasa lafiya tiyata a asibiti da kansa (Hoto)

Wani aikin tiyata daya gagari kundila yayi sanadiyyar komawa dakin tiyata da ministan lafiya Farfesa Isaac yayi domin gudanar da aikin tiyatan da kansa dan ceto rayuwar mata masu dauke da cutar yoyon fitsari.

Daily Trust ta ruwaito wannan aiki ya gudana ne a karkashin shirin tallafi da wata kungiyar kula da masu cutar yoyon fitsari dake kasar Amurka ta bayar don yima matan aikin.

KU KARANTA: Kalli yadda Ali Nuhu ya taka rawar gani a cikin wani ƙayataccen Fim ɗin Turanci

A yayin tiyatan, anyi ma sama da mata 33 aikin tiyatan, sa’annan an tantance mata da dama da za ayi ma wannan aiki a satin mai zuwa.

Cutar yoyon fitsaro: Ministan Lafiya yayi ma marasa lafiya tiyata a asibiti da kansa (Hoto)
Ministan Lafiya a dakin tiyata

Tun a baya dama ministan lafiya ya nuna sha’awar sa na sa hannu cikin wannan aikin yi ma mata masu dauke da ciwon yoyon fitsari tiyata, musamman idan ayyukan sun yi ma likitocin da aikin ya rataya akansu yawa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cikin mata 12,000 dake dauke da ciwon, mata 5000 kacal ake iya gyara su, wannan ne ya sanya ministan daukan alwashin lallai sai an cigaba da wannan aiki domin warkar da sauran matan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Yadda ruwan sama yaci gidajen mutane, kalla:

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel