Ba da mu ba: Jihohi 3 a Najeriya da su ka ce a daina jefa su cikin ‘Yan Biyafara

Ba da mu ba: Jihohi 3 a Najeriya da su ka ce a daina jefa su cikin ‘Yan Biyafara

- Jihar Ribas da kuma Jihar Benuwe sun ce ba su cikin Biyafara

- Yankin Neja-Delta mai ma fetur ma dai sun ce babu su a ciki

- Kasar Inyamurai ne dai kurum ake so a bari cikin Biyafara

Dama kun ji cewa Mutanen Jihar Ribas da Benuwe sun ja kunnen jagoran Kungiyar IPOB ta Biyafara watau Nnamdi Kanu inda su kace idan yana haukan sa ya daina hadawa da su. Haka Yankin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan na Neja-Delta ma dai sun ce babu su a ciki.

Ba da mu ba: Jihohi 3 a Najeriya da su ka ce a daina jefa su cikin ‘Yan Biyafara
Hoton jagoran yan Biyafara a gaban Kotu

1. Yankin Ijaw na Neja-Delta

Mutanen Kabilar Ijaw Neja-Delta sun ce babu su a cikin maganar Biyafara da Nnamdi Kanu yake ta fafatuka. Wani Shugaban Matasan Yankin ya bayyana haka kwanan nan.

KU KARANTA: Su Nnamdi Kanu sun ce Buhari ya rasu

Ba da mu ba: Jihohi 3 a Najeriya da su ka ce a daina jefa su cikin ‘Yan Biyafara
Jama'a da dama sun yi tir da yunkurin Kanu

2. Jihar Ribas

Har Fadar Sarkin Musulmi Gwamnan Jihar Ribas Nyesom Wike ya je inda ya kara tabbatar da cewa ba su da hadi da Biyafara. Nnamdi Kanu ya dai ce Jihar ce ma za ta zama babban Birnin Biyafara idan an raba kasar.

3. Jihar Benuwe

Wasu manyan Jihar na Benuwe sun ma yi kaca-kaca da Nnamdi Kanu inda har wani yace ya kamata a leka da Kanu wajen Likita.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ko za ka iya barin Najeiya zuwa wata kasa?

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng