Boko Haram sun kashe shugaban mafarautan Adamawa, da wasu mutane 3
- Bukar Jimeta ya rasu ne a yayinda suke gwabza fada da mayakan Boko Haram a kauyen Dagu
- Bukar ya kashe mayakan Boko Haram da dama kafin su samu galaba a kansa
- Anyi jana’izar Bukar a ranar Lahadi da yamma a garin Gombi
A ranar asabar da ta wuce ne, mayakan Boko Haram suka kashe shugaban mafarauta na jihar Adamawa, Bukar Jimeta tare da wasu mafarautan guda uku.
Wata majiya tace an kama su Bukar din ne a kauyen Dagu wanda ke da iyaka da Askira Uba a jihar Borno a yayin da suke kokarin kare wata hari da yan Boko Haram din suka kawo a kauyen.
Wani mafaraucin da ya samu ya tsira da ransa yace mayakan Boko Haram sun kawo hari a kauyen amma mafarautan sun kora su.
DUBA WANNAN: Fadar shugaban kasa ta fadi wanda zai lashe zaben 2019 idan anyi
“Mun gwabza yaki dasu sosai har sai da makaman mu suka kare. Mun so mu gudu amma shugaban mu yace mu cigaba da fadan. Ganin cewa yan Boko Haram din suna da makamai masu karfi sosai yasa wasun mu suka gudu amma shugabanmu Bukar Jimeta ya cigaba da gwabza fadan da su.
“Ganin sun kasa kashe shi da bindiga, sai suka yi amfani da gatari suke sare shi. Yadda akayi ya rasu kenan. Hakika, mun yi rashin jarumi,” Inji majiyar da baza mu iya fadar sun aba saboda tasro
Mazauna kauyen sunce karan harbin bindiga ne ya tashe su daga barci a daren ranar asabar.
“Mafarautan nan ne suke taimaka wa wajen kawar da sauran mayakan Boko Haram da suka rage, suna kawo farmaki ne domin su sace kayan abinci da kuma shanu,” inji wani mutum mai suna Umaru wanda ke hanyar sa ta tsere wa daga garin.
“Wannan karan, mayakan Boko Haram din su zo da yawa sanye da kayan sojoji. Bukar Jimeta da sauran mafarauta ne gwabza fada da su.
“Ya kashe yan Boko Haram din da yawa kafin su kashe shi, akwai alamar saran gatari mai zurfi a jikin gawarsa,” inji shi
Shugaban kungiyan mafarauta na Adawama ya tabbatar da faruwa lamarin a hirar wayan tarho.
“Munyi babban rashi amma baza mu karayya ba, zamu cigaba da kare garuruwan mu.”
Aisha Gombi, shugaban mata mafarauta ta nuna bacin ranta akan rasuwar Jimeta, tace ya nuna jarumtaka matuka a wajen yaki da yan Boko Haram.
Anyi jana’izar Jimeta a ranar lahadi da yamma a garin Gombi. Tun shekara ta 2014 ne dai mafarauta da kuma yan banga suke hadin gwiwa da soji da ma sauran jami’an tsaro dimin yaki da yan Boko Haram a Arewa maso gabashin Najeriya.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng