Assha! Wani mai sana'ar walda ya dirka wa wata matar aure ciki a Abuja
1 - tsawon mintuna
Wata kotu dake a garin Abuja babban birnin tarayya ta bayar da belin wani mai sana'ar walda wanda yake da suna Abubakar Sadiq akan kudi Naira 30,000 bayan da aka kama shi da laifi dumu-dumu na yi wa wata matar aure ciki.
Wannan al'amari dai ya auku ne a garin Abuja kuma mijin matar mai suna James olanga shine ya shigar da karar a kotun dake zaman nata a Abuja.
Legit.ng dai ta samu labarin cewa wanda ake zargin ya amasa laifin sa amma kuma sai ya shaidawa kotun cewa shi bai san tana da aure ba shi yasa.
Yace fadawa kotun cewa sun hadu ne a matsayin su na baligai in da suka fada kogin soyayya amma bai taba sani cewa wai tana da aure ba.
Asali: Legit.ng