Dandalin Kannywood: Yadda ake kwanciya da mata kafin a saka su fim - Wata jaruma
Mutane da dama dai dama ba tun yau ba suna kokawa da yadda masana'antar fim din Hausa ta Kannywood ke gurbata tarbiyya da al'adun malam Bahaushe.
Baya ga haka ma dai wasu na yiwa yan fim din kallon wasu bata gari inda ake yi wa da yawa daga cikin matan kallon wadanda ke saida budurcin su a farfajiyar masana'antar ta fim.
Legit.ng ta tsinkayi wata jaruma mai suna Khadija Abubakar Mahmood a cikin wata fira da tayi da mujallar 'fim' tana cewa tabbas hakan yana faruwa amma fa ga wadda ta yadda.
A cikin firar dai an tambaye ta ne ko wani ya taba tunkarar ta da magana makamanciyar wannan sadda ta shigo masana'antar inda ta kada baki tace ita babu wanda yayi mata haka.
Daga nan ne kuma sai ta ba mata yan uwanta shawar cewa suyi taka tsantsan don kada su fada hannu yan damfarar fin din.
Asali: Legit.ng