Masu min kallon jahili zasu sha mama nan kusa – A Zango

Masu min kallon jahili zasu sha mama nan kusa – A Zango

- Shararren dan wasan Hausa Fim Adam Zango zai koma karatu

- Zango yace shi ba dan Luwadi bane

Jarumin fina finan Kannywood, Adam Zango yace babban burinsa a rayuwa bata wuce ya kara ilimi wajen magana da harshe Turanci ba, kamar yadda ya shaida ma gidan rediyon BBC Hausa.

Shahararren dan wasan, ya bayyana cewar ya kusan dakatar da harkar Fim, inda yake bukatar daga mata kafa domin ya koma makaranta domin karo karatu, musamman yanzu da wasu ke mai kallon jahili.

KU KARANTA: Buhari zai dawo nan ba da dadewa ba – Tinubu

Bugu da kari, domin ya tabbatar da burinsa a rayuwa tare da yi ma kansa shiri mai kwari, A Zango ya dauki hayar wani Malamin gida, wanda ke yi masa bitan karatu.

Masu min kallon jahili zasu sha mama nan kusa – A Zango
A Zango

“Nayi karatun Boko, sa’annan ina da ilimin addini, kuma a yanzu haka ina son cigaba da karatu na, akalla in samu kwalin Difloma, amma burina shine na iya Turanci sosai da sosai.” Inji A Zango.

Dangane da zargin luwadi da ake yi masa kuwa, A Zango ya bayyana ma majiyar Legit.ng cewa shi ba dan Luwadi bane, kuma bai taba luwadi ba, sa’annan wannan zargi mara tushe na bata masa rai, wanda ya taba janyo hana bashi matar aure.

Legit.ng ta tattaro bayanai cewa an haifi jarumi a garin Zangon Kataf na jihar Kaduna, sa’annan ya girma a garin Jos.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Zaka iya taimakon Buhari idan ya bukata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng