Shekaru 10 da auren Sani Danja: Ya nuna farin cikinsa cikin wasu kyawawan hotuna

Shekaru 10 da auren Sani Danja: Ya nuna farin cikinsa cikin wasu kyawawan hotuna

- Matar Sani Danja, Mansura Isah da mijinta sun yi murnan cikar shekaru 10 da aure

- Yan wasan Kannywood din sun bayyana hotunan yayansu

Shahararren dan wasan Kannywood Sani Danja tare da tsohuwar tauraruwar Kannywood Mansura Isah sun yi bikin cikar shekarunsu 10 da aure a ranar Alhamis 13 ga watan Yuli.

A shekarar 2007 ne Danja ya angwance da Mansura Isa, kuma cikin ikon Allah, Allah ya azurtasu da yaya 4, mace daya da maza 3.

KU KARANTA: Rundunar Sojin sama da sabunta wasu jiragen leken asiri masu sarrafa kansu (HOTUNA)

Babbar yarsu sunanta Khadijatul Iman, sai Khalifa Sani, Yakubu da kuma Yusuf, kamar yadda majiyar Legit.ng, jaridar Rariya ta ruwaito.

Shekaru 10 da auren Sani Danja: Ya nuna farin cikinsa cikin wasu kyawawan hotuna
Sani Danja da iyalansa

A yanzu haka dai Sani Danja ya shahara ba’a fannin wasannin Kannywood ba kadai, har ma da fannin wake wake, tallace tallace da kuma fina finan Turanci.

Ga sauran hotunan a nan:

Shekaru 10 da auren Sani Danja: Ya nuna farin cikinsa cikin wasu kyawawan hotuna
Sani Danja da Mansura

Shekaru 10 da auren Sani Danja: Ya nuna farin cikinsa cikin wasu kyawawan hotuna
Sani Danja

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

An bude tashar Yanya: Kalla

Asali: Legit.ng

Online view pixel