Dandalin Kannywood: Matar Jarumi Sadiq Sani Sadiq ta haifi sambaleliyar budurwa (Hotuna)

Dandalin Kannywood: Matar Jarumi Sadiq Sani Sadiq ta haifi sambaleliyar budurwa (Hotuna)

- Jarumi Sadiq Sani Sadiq ya samu karuwa

- Ya rada wa jaririyar suna Asma'u

- Yanzu yayan jarumin biyu kenan

Labarin da muke samu yana nuna mana da cewa fitaccen jarumin wasannin fina-finan Hausa na Kannywood watau Sadiq Sani Sadiq ya samu karuwa da diya mace a ranar asabar din da ta gabata.

Matar jarumin Marja Shehu Shema ce dai ta haifar masa da sambaleleiyar budurwar a farkon karshen makon.

Dandalin Kannywood: Matar Jarumi Sadiq Sani Sadiq ta haifi sambaleliyar budurwa (Hotuna)
Dandalin Kannywood: Matar Jarumi Sadiq Sani Sadiq ta haifi sambaleliyar budurwa (Hotuna)

Legit.ng dai ta tuna cewa a farkon shekarar 2013 ne dai aka daura auren jarumin da matar ta sa Murja wadda take zaman kanwar tsohon gwamnan jihar Katsina Ibrahim Shehu Shema a garin Katsina.

Yanzu haka dai yayan jarumin sun kama biyu kenan bayan wannan haihuwar. Tuni dai har ya radawa jaririyar suna Asma'u.

Asali: Legit.ng

Online view pixel