Babu abinda mai gidana yake bukata a halin yanzu, kamar addu'ar 'yan Najeriya - Aisha Buhari
Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha Buhari ta bayyana cewa a halin da ake ciki babu abun da maigidan ta ke bukata da ya wuci adduán ýan Najeriya.
A cewar majiyarmu ta Hausa press 24, uwargidan shugaban kasar, t ace maigidanta ya shaida mata cewa zai mutu da bakin ciki idan har bai samu cikakkiyar lafiyar da zai cika alkawaran da ya dauka ma alúmman Najeriya ba.
Sannan kuma ta ce shugaban kasar yace yana tsoron abinda ka iya zuwa ya dawo a Najeriya idan ta Allah ta kasance a kansa. Sai dai uwargidan shugaban kasar ta ce shugaban kasar ya samu sauki sosai, sannan ta roki ýan Najeriya da su ci gaba da yi masa adduán samun lafiya.
Aisha Buhari ta ce: “Babu abinda mai gidana yake bukata a halin yanzu, kamar addu'ar 'yan Najeriya, domin ya shaida min cewa zai mutu da bakin ciki idan har bai samu cikakkiyar lafiyar da zai cikawa 'yan Najeriya alkawarin da ya daukar musu ba.
KU KARANTA KUMA: An dakatar da Shugaban hukumar NHIS, kan zargin aikata zamba
"Sannan kuma ya shaida min cewa, yana tsoron abinda zai je ya dawo a Najeriya, idan ta Allah, ta kasance gare shi amma naga jikin nashi akwai sauki sosai saboda haka ina rokon 'yan'uwana 'yan Najeriya, Musulmi da Kirista, da-su-ci gaba da yiwa mai gidana addu'ar samun lafiya.“
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng