Dandalin Kannywood: An nada Ali Nuhu Sarki, Halima Atete Sarauniya

Dandalin Kannywood: An nada Ali Nuhu Sarki, Halima Atete Sarauniya

- Yanzu dai Ali Nuhu shine Sarkin Kannywood

- Haka ma Halima Atete ita ce Sarauriyar Kannywood

- Anyi wannan nadin ne a garin Bauchi da Kano

Anyi wani kwarya-kwaryan taron biki wanda matasan Kannywood suka gabatar karkashin jagorancin Alhasan Kwalli inda suka karrama fitattun jarumai na masana'antar Kannywood.

A wajen taron da aka gudanar a garuruwan Bauchi da Kano dai kungiyar ta karrama jarumi Ali Nuhu a matsayin sarkin Kannywood yayin da iya kuma Halima Atete aka nada ta a matsayin sarauniya duk dai ta masana'antar.

Dandalin Kannywood: An nada Ali Nuhu Sarki, Halima Atete Sarauniya
Dandalin Kannywood: An nada Ali Nuhu Sarki, Halima Atete Sarauniya

Legit.ng ta samu labarin cewa an gudanar da zaben ne bisa saka kuri’a da masu jagorantar kungiyar kannywood suka yi, sun la’akari da abubuwa masu tarin yawa kafin su zabi Halima Atete amatsayin sarauniyar kannywood, babban abinda aka duba shine gudumawar da ta bayar tun lokacin da ta shigo masana’antar hausa fim.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel