An kama wadanda ake zargi da kashe Abdulhakim Bauchin Bauchi
- Rundunar 'yan sanda reshen jihar Bauchi ta samu nasarar kama karin wasu daga cikin wadanda ake zargi da kisan Abdulhakim Bauchin Bauchi
- Rundunar tace an samu nasarar kama mutanen ne a sakamakon tsaurara matakan tsaro da aka yi a jihar
Rundunar 'yan sanda reshen jihar Bauchi ta samu nasarar kama karin wasu daga cikin wadanda ake zargi da kisan Abdulhakim Bauchin Bauchi.
A wata sanarwa da rundunar ta fitar dauke da sanya hannun, DCP Chris Owolabi, tace ta kama mutanen cikin motar margayin kirar Mercedes Benz 300.
Rundunar tace an samu nasarar kama mutanen ne a sakamakon tsaurara matakan tsaro da aka yi a jihar a sakamakon bukukuwan sallah.
KU KARANTA KUMA: Korar 'yan kabilar Igbo: Gwamnan Kano, Ganduje ya yi magana kan makomar ýan Igbo
Idan dai ba'a manta ba an yi wa margayi Abdulhakim Bauchin Bauchi kisan gilla ne a ranar 12 ga watan Maris 2017.
A wani al'amari na daban Legit.ng ta rahoto inda ta yi karo da wani labari mai karya zuciya na wani karamin yaro da malamin sa ke azabatar da shi.
A cewar wani mai amfani da shafin Facebook, yaron mai suna Hassan ya ce mahaifinsa wanda a yanzu ya rasu shine ya tura sa karatu gurin mutumin.
A yanzu jami’an yan sandan jihar Gombe sun kama malamin dake koyar da karamin yaron.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng