Ka ji abin da Shugaban Real Madrid ya fada game da Ronaldo

Ka ji abin da Shugaban Real Madrid ya fada game da Ronaldo

– An batawa Dan wasan Real Madrid rai Inji Shugaban Kulob din

– Duk da haka Cristiano Ronaldo ba zai tashi ba Inji Perez

– Florentino Perez ya tabbatar da cewa ran Dan wasan ya baci

Ku na sane cewa ana zargin ‘Dan wasan da kin biyan haraji . Wannan zargi bai yi babban ‘Dan wasan dadi ba ko kadan. Shugaban Kulob din na Madrid yace amma ‘Dan wasan na nan.

Ka ji abin da Shugaban Real Madrid ya fada game da Ronaldo
An batawa Dan wasa Cristiano Ronaldo rai Perez

Kwanaki dai mu ka kawo maku rahoto cewa Dan wasa Cristiano Ronaldo na iya tashi daga Kungiyar Real Madrid bayan an fara zargin sa da kin biyan wasu kudin haraji a Kasar Sifen wanda wannan zargi ya bata masa rai.

KU KARANTA: Ana korar masu zaman kan su daga Abuja

Ka ji abin da Shugaban Real Madrid ya fada game da Ronaldo
Chile ta yi waje da Portugal a finariti

Shugaban Kulob din Florentino Perez ya tabbatar da cewa ‘Dan wasan bai ji dadin abin da ya faru ba amma kuma duk a je a dawo ba zai sa ya tashi daga Real Madrid ba. Nan da wata mai zuwa dai za a shiga Kotu da ‘Dan wasan.

Kamar yadda mu ka samu labari kwanaki daga Jaridar Daily Mirror ‘Dan wasan yace dole sai Real Madrid ta biya kusan Dala Miliyan 16 da ake zargin sa da kin biya domin haraji domin ya cigaba da takawa Kungiyar leda.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wuta ya tashi a wani gida [Bidiyo]

Asali: Legit.ng

Online view pixel