Toh fa: Sarkin Kano ya dakatar da ɗan tsohon Sarki Bayero kan rashin biyayya

Toh fa: Sarkin Kano ya dakatar da ɗan tsohon Sarki Bayero kan rashin biyayya

- Sarkin Kano ya dakatar da hakimin karamar hukumar Takai daya daga cikin dan tsohon Sarkin Kano Ado Bayero

- An samu Hakimin da laifin nuna reni ga Sarkin Kano Muhammadu Sanusi 11

- Mazarautar ta bukaci dan tsohon Sarkin Kano ya gurfana a gaban ta

Sarkin Kano, mai martaba Malam Muhammadu Sanusi 11, ya dakatar da wani dan tsohon Sarkin Kano Alh. Ado Bayero a kan rashin biyayya.

Dan tsohon Sarkin da aka dakatar shi ne Alhaji Bashir Ado Bayero, Hakimin karamar hukumar Takai.

An bukaci hakimin da aka dakatar da ya bayyana gaban kwamitin da'a na fadar kafin a san mataki na gaba da za a dauka.

Toh fa: Sarkin Kano ya dakatar da ɗan tsohon Sarki Bayero kan rashin biyayya
Sarkin Kano, mai martaba Malam Muhammadu Sanusi 11

A halin yanzu, Sarki Sanusi ya nada Alhaji Mahmud Shattima a matsayin na wucin gadi wanda zai shugabanci gundumar har zuwa lokacin da kwamitin da'a zata fitar da shawarwari .

Bashir Ado Bayero ne na biyu a cikin ɗan marigayi sarkin da za a kwace ikon tun rasuwar mahaifinsu. Na farko dai shi ne Ciroman Kano, Alhaji Sanusi Ado Bayero, wanda aka cire a watan Oktoba 28, 2015 a kan irin wannan laifin.

Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban ma’aikatar masarautar, Alhaji Munir Sanusi, ya ce dakatar da Bayero ya biyo bayan reni da hakimin yayi wa sarki Sanusi a lokacin zaman taron fadar.

KU KARANTA: Hudubar Idi: Ka ji kiran da wani Limami yayi kira ga ‘Yan Najeriya

Wannan abin ya faru ne a lokacin da Hakimin ya zo fada neman izinin tafiya zuwa Saudi Arabia domin zuwa duba lafiyarsa, bayan da Sarkin ya amince masa da bukatarsa, sai ya mika sunan mutumin da yake so ya wakilce shi bayan tafiyarsa.

Amma Sarki Sanusi ya ki amincewa da sunan da ya bayar, a nan ne shi Hakimin ya nuna rashin kunyarsa ga Sarkin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon inda mai martaba sarki Sanusi ya shawarci shugabannin Najeriya da shugabanci na nagari

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng