Shugaba Buhari ya aikawa 'yan Najeriya sakon barka da Sallah
- A cikin sakon sallar shugaban kasa Buhari ya bukaci ‘yan Najeriya da su zauna lafiya da juna su yi watsi da duk wani furucin da zai jawo tashin hankali
- Buhari ya ce ‘yan Najeriya su gode ma Allah da ya sa suka ga karshen Ramadan lafiya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aikawa musulmai da kiristocin Najeriya sakon gaisuwa a yayin bikin sallah, inda ya yi kira ga dukkan 'yan Najeriya da su zauna lafiya da juna su yi watsi da duk wani furucin da zai jawo tashin hankali.
KU KARANTA KUMA: YANZU-YANZU: An ga wata a Adamawa, Sokoto da Katsina - Sarkin Musulmai, Abubakar Sa'ad
Sakon na rubuce ne kama haka:
"Ina mai godiya ga Allah da muka kammala wannan watan Azumi na Ramadan. Ina mika sakon gaisuwa ga dukkan musulman Nijeriya da 'yan uwanmu Kiristoci a yayin bikin sallah.
"Allah ya sa mu dore kan darrusan da muka dauka a cikin watan na Ramadan, kamar tausasawa, yawaita ibada da sauransu.
"Ina kara jan hankalin 'yan Nijeriya da su kauracewa duk wasu kalamai da za su jawo tashin hankali a kasar nan. Mu zauna lafiya mu hada kai wanda shine silar ci gaban kowace kasa.
"Barka da sallah"
Sanarwa daga maitamakwa shugaba Buhari kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu.
Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng