Manyan ‘Yan wasa 3 da aka kama da laifin haraji

Manyan ‘Yan wasa 3 da aka kama da laifin haraji

– Ana zargi Dan wasan Real Madrid bai biya wasu kudin haraji ba

– Haka kuma ‘Dan wasa Di-Maria ya tabbatar da bakin sa yayi laifi

– Bayan wadannan dai akwai da dama da ake bincika ko aka gama

Bayan Cristiano Ronaldo an samu ‘Yan wasa da dama da ake zargi da laifi wajen biyan haraji. Tuni aka samu wasu da laifi wasu kuma watakila su tsira. Ga dai jerin ‘Yan wasan:

KU KARANTA: 'Yan Sandan Najeriya sun yi wawan kamu

Manyan ‘Yan wasa 3 da aka kama da laifin haraji
‘Yan wasa 3 da aka kama da laifin haraji

1. Lionel Messi

Kwanaki Kotu ta yankewa shararren Dan wasa Lionel Messi daurin watanni 21 bayan an same sa da laifin kin biyan haraji har na kusan Dalar Euro Miliyan 3.5 daga shekarun 2007 zuwa 2009. Dan wasan dai ba zai yi zaman kaso ba.

Manyan ‘Yan wasa 3 da aka kama da laifin haraji
Di-Maria bai biya wasu kudin haraji ba a Sifen

2. Cristiano Ronaldo

Ana zargin ‘Dan wasan Duniya Ronaldo da kin biyan kusan Dala Miliyan 16 ga Hukuma wanda hakan ta sa ya fusata a Real Madrid.

Manyan ‘Yan wasa 3 da aka kama da laifin haraji
Ana zargin Dan wasan Real Madrid da rashin gaskiya

KU KARANTA: Fitaccen Dan wasan Hausa zai yi aure

3. Angel Di-Maria

Shi ma Dan wasan PGS Di-Maria an same sa da laifin rashin biyan kudin haraji a lokacin da yake kasar Sifen kuma ya amince cewa yayi ba daidai ba hakan ta sa ya samu hukuncin shekara guda, shi ma ba zai zauna a kurkuku ba.

Akwai dai sauran ‘Yan wasa irin su Luka Modric da ake tuhuma da Javier Mascherano da tuni Kotu tayi ram da shi. Tauraron Dan wasa Neymar Jr. shi ma ba a bar sa a baya ba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin har yanzu Najeriya ce uwar tafiya a Afrika

Asali: Legit.ng

Online view pixel