Danjuma da Danjumai: ‘Yan Darika da ‘Yan Shi’a ‘Yan uwa ne Inji Shehun Tijjaniyya

Danjuma da Danjumai: ‘Yan Darika da ‘Yan Shi’a ‘Yan uwa ne Inji Shehun Tijjaniyya

– Babban Shehin Darika Dahiru Bauchi yayi magana game da Shi’a

– Shehun Darikar yace su da ‘Yan Shi’a ‘Yan uwan juna ne

– Dahiru Bauchi yace sun yi tarayya da ‘Yan Shi’a wajen son Manzon Allah

Sheikh Dahiru Bauchi yace ba su fada da ‘Yan Shi’a. Shehin ya fadi haka ne yayin da aka kai masa ziyara. ‘Yan Shi’a da Dariku su na kaunar Manzo Inji Shehin.

Danjuma da Danjumai: ‘Yan Darika da ‘Yan Shi’a ‘Yan uwa ne Inji Shehun Tijjaniyya
Darika da ‘Yan Shi’a ‘Yan uwa ne-Dahiru Bauchi

Babban Shehin Darika Tijjaniyya Dahiru Usman Bauchi ya bayyana cewa ‘Yan tarika da ‘Yan Shi’a duk jirgi daya ne ya dauko su don kuwa sun yi tarayya wajen kaunar Manzon Allah Muhammadu SAW.

KU KARANTA: Yadda aka yi da dabinon Kasar Saudiya

Danjuma da Danjumai: ‘Yan Darika da ‘Yan Shi’a ‘Yan uwa ne Inji Shehun Tijjaniyya
Sheikh Dahiru Bauchi yayi magana game da Shi’a

Wasu ‘Yan Kungiyar Shi’a ne dai su ka kai masa ziyara bayan ya kammala karatun tafsirin bana. Ya yabawa ‘Yan Shi’ar wanda yace duk sun hadu wajen soyayyar Manzon Allah da iyalan sa. Shehin dai ya yabawa wannan ziyara da aka kai masa a Kano.

Ku na sane cewa Manzon Allah SAW ya tabbatar da cewa za a dace da daren nan na Laylatul Qadr mai albarka a cikin ‘yan kwanakin nan na 10 na karshen watan Ramadan inda ake kasafin duk wani alheri a shekarar.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda wani mai garkuwa da mutane ya zama mai kudi

Asali: Legit.ng

Online view pixel