Wasanni: Dattawan Barca za su kara da na Manchester United

Wasanni: Dattawan Barca za su kara da na Manchester United

- Tsoffin 'yan wasan Barcelona za su kara da na Manchester United a wasan sada zumunta a ranar 30 ga watan Yuni.

- Za a yi wasan ne domin tara kudi don taimaka wa masu fama da cutar daji a cibiyar Barcelona da ke Camp Nou.

Tuni kocin tsoffin 'yan wasan Barcelona, Jose Mari Bakero ya kara mika goron gayyata ga Ronaldinho da Edgar Davids da kuma Simao Sabrosa bayan wadanda ya gayyata.

Wasanni: Dattawan Barca za su kara da na Manchester United
Wasanni: Dattawan Barca za su kara da na Manchester United

Legit.ng ta samu labarin cewa wadanda za su buga wa Barcelona karawar sun hada da Angoy da Guzman da Juan Carlos da Popescu da Nadal da Belletti da Andersson da Dehu da Edmilson da Goikoetxea da Mendieta da Giuly da kuma Julio Salinas.

'Yan wasan da aka tabbatar za su buga wa Manchester United sun hada da Blomqvist da Fortune da Poborsky da Berbatov da Ji Sung Park da Silvestre da kuma Dwight Yorke.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel