Jama’a na bautan wani yaro ‘mai bindi’ a kasar India (HOTUNA/BIDIYO)
- An haifi wani yaro a kasar India da bindi
- Jama'a sun shiga harkar bautan wannan yaro
Wani karamin yaro dan shekara takwas mai suna Dulha Singh da aka haifa da wani abu kamar bindi a bayansa ya samu mabiya masu bauta masa.
Bindin wannan yaron ya samu asali ne daga wani tarin gashi da ya fito ma yaron a bayansa, sa’annan iyayensa sun ce yanke wannan bindi ka iya zama mummunan laifi akan wanda zai iya zuwa da mummunan sakamako.
KU KARANTA: Mutane 6 sun mutu, 20 sun jikkata a yayin gobarar bene mai hawa 27 (Hotuna)
A yanzu haka yan kauyen Amritsar, inda Dulha ke zaune da kawunsa suna tururuwa gidansa domin yi masa bauta, a yadda suke fada, sunce Dulha kwatankwancin ubangijin birai ne na addinin Hindu mai suna Hanuman.
Dayake yaro Dulha na sha’awar hawa bishiya da wasa a akai, yasa ya kara tabbatar ma yan kauyen cewa lallai shine ubangijin birai na addinin Hindu.
Wannan yasa yan kauyen suke ganinsa kamar wata rahama ne a garesu, shi yasa ma suke shafarsa domin samun tubarraki.
Wasu kuma bindin nasa suke tabawa domin samun babban tabarraki, da karama, innarsa tace “Jama’a da daman a zuwa ganinsa a kullum, sun yi amanna shine Hanuman Ji.”
Sai dai Legit.ng ta ruwaito yaro Dulha baya jin komai a jikinsa, kuma baya damuwa da yadda jama’a ke son taba shi da taba bindin nasa, shi kam bai ma san dalilin da yasa jama’a ke son neman tubarraki a wajen sa ba.
Ga bidiyon yaron nan:
Kalli abinda wata yarinya yar Najeriya keyi da jikinta:
Asali: Legit.ng