Dandalin Kannywood: An suburbudi matashi Ado Gwanja? (Hoto)

Dandalin Kannywood: An suburbudi matashi Ado Gwanja? (Hoto)

Kwanakin baya ne rahotanni ke cewa fitaccen dan wasan kanywood wanda ya shahara wajen fitowa a matsayin dandaudu wato Ado Gwanja yasha duka a hannun jami’an yan sanda dake caji ofis din Yar Akwa dake Kano.

Gwanja ya ziyarci caji ofis dinne domin ya karbi belin wani yaronsa da aka kama mai suna chasis da aka kama da laifin yawon dare , amma sai jami’an tsaron suka bukaci ya biya kudin beli naira dubu goma, nan fa yace babu abinda zai biya a beli kyauta ne.

“Hakan ya jawo hayaniya tsakanin yansanda da kuma Gwanja, ” daya daga cikin jami’an tsaro.

Dandalin Kannywood: An suburbudi matashi Ado Gwanja? (Hoto)
Dandalin Kannywood: An suburbudi matashi Ado Gwanja? (Hoto)

Legit.ng ta samu labarin cewa ganin rikicin yaki karewa da maigidansa shine chasis ya saka baki a rikicin, ai kuwa jami’an tsaro suka ce da wa Allah yahada mu nan suka shiga dukansa.

A cewar daya daga cikin jami’an tsaron dake wajen da Gwanja yaga dukan yana nema ya wuce misali shine ya nemi shiga tsakani aikuwa sai suka hada dashi har takai da sunji masa ciwo.

Abin jira a gani shine ko rundunar yansandan jihar Kano zata biwa Gwanja da yaronsa hakkinsu na yi musu duka ba tare da sun aikata laifin komai ba.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel