Paul Pogba ya gana da Limamin Masallacin Annabi dake Madina (Hotuna)
- Paul Pogba ya samu ganawa da babban limamin masallacin Annabi
- Pogba yayi wannan ganawa ne da Sheikh Ali Bin Abdur Rahman Al Hudhaify
Shahararen dan wasan kwallon kafa dan kasar Faransa dake taka leda a kungiyar Manchester United, Paul Pogba ya samu ganawa da babban limamin masallacin Annabi dake Madina. Inji rahoton BBC Hausa.
Pogba yayi wannan ganawa ne da Sheikh Ali Bin Abdur Rahman Al Hudhaify, wanda shine babbban Limamin Masallacin yayin ziyarar Ibadan Umara daya kai a cikin wannan watan Azumin Ramadana.
KU KARANTA: Alhamdulillah: Musulunci ya samu ƙaruwa
An hangi Pogba da Limanin suna gaisawa tare da nuna farin cikin saduwa, sa’annan sun samu wani dan lokacin sun tattaunawa, sai dai ba’a san menene ginshikin abubuwa da suke tattaunawa ba.
Idan ba’a manta ba Legit.ng ta kawo muku wani rahoton raba gardama dake fayyace matsayin Musluncin Pogba, inda muka bayyana muku cewa tabbas Pogba Musulmi ne kuma ya dauki addini da muhimmanci.
Sai dai ba Pogba bane kadai Musulmi a cikin yan kwallo, inda akwai irin su Mesul Ozil na Arsenal, Ahmed Musa na Leicester, Arda Turan na Barcelona, Kareem Benzema na Real Madrid, Emre Can na Liverpool, Musa Dembele na Tottenham da sauransu.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Yadda direban Fasto ya karbi Musulunci
Asali: Legit.ng