An kashe 'Yan Sanda a wajen wani mugun rikici da Sojoji
– Sojojin Najeriya sun kai wa ‘Yan Sanda hari a Garin Kalaba
– Ba mamaki wasu manyan Jami’an ‘Yan Sanda sun rasa ran su
– Abin ya kai har an kona ofishin ‘Yan Sanda
Rikicin Sojoji da ‘Yan Sanda ya bar gawawwaki Jami’ai da dama
An yi fada ne tsakanin ‘Yan Sanda da Sojojin ruwa
Daga baya dai Sojojin sama da kasa su ka shigo ciki
Mun samu labari daga kafafe da dama cewa jiya da dare an yi wani mugun fada tsakanin ‘Yan Sanda da Jami’an Sojoji wanda yayi sanadiyar mutuwar wasu ‘Yan Sanda. Majiyar mu tace an fara rikicin ne da Sojojin ruwa daga baya sauran Sojoji su ka kutso ciki.
KU KARANTA: An kashe wasu manoma har 3 a Taraba
Wanda ya ji yadda abin ya faru cikin dare ya bayyanawa Legit.ng cewa an kona ofishin ‘Yan Sanda. Abin dai ya kai an bude barikin Sojoji kowa ya dauki manyan makamai inda aka shiga budawa ‘Yan Sandan wuta. An dai ce an harbi wani Sojan ruwa ne a hannu.
Yayin da mutanen Yankin Biyafara ke kokarin tunawa da mutanen su da su ka kwanta dama a lokacin Yakin Basasa, Sojojin Najeriya sun budawa mutanen Biyafara wuta a Garin Aba da ke Jihar Abia kwanakin baya kamar yadda mu ka ji.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ko Jama'a sun goyi bayan mulkin Soji?
Asali: Legit.ng