Dandalin Kannywood: Kunji dalilin da yasa aka sassari Jarumi Aminu Sharif Ahlan

Dandalin Kannywood: Kunji dalilin da yasa aka sassari Jarumi Aminu Sharif Ahlan

- Miliyoyin mutane a fadin duniya sun ga hotunan da mutane da jaridu suka buga ina jike cikin jini sanadiyyar sara har waje biyar da wasu azzalumai suka yi yunkurin halaka ni.

- Amma ba wanda ya san zahirin dalilin kisan da aka kusan yi min.

Legit.ng ta samu labarin cewa jita jita da shaci fadi kawai ake, wasu su ce sata aka zo yi min. Wasu su ce ai makiya ne da na tsonewa ido da dai dalilai barkatai.

Gaskiyar abun da ya faru shine:

Ina zaune wajen 11 na dare a kofar gidana da na koma a unguwar Ja’en dake Kano, kusa da layin shago tara.

Dandalin Kannywood: Kunji dalilin da yasa aka sassari Jarumi Aminu Sharif Ahlan
Dandalin Kannywood: Kunji dalilin da yasa aka sassari Jarumi Aminu Sharif Ahlan

Sai ga mutane tsaye kai na da makamai suka kama sarana, karshe suka ce min sun ga rubuce-rubace na da kuma banner da na yiwa gwamna, wanda M.D na RIWASA ya dauki nauyi.

Kuma sun gargade ni cewa nan gaba kashe ka za mu yi.

Fitowar mutane yasa suka gudu.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita:

Asali: Legit.ng

Online view pixel