Wata mata ta kona mijinta da amaryarsa saboda bakin kishi a Arewa

Wata mata ta kona mijinta da amaryarsa saboda bakin kishi a Arewa

- Wani Mazaunin Unguwan Hayin Na-iya dake Jihar Kaduna mai suna Suleiman Kero ya gamu da ajalinsa bayan ya kara aure na biyu.

- Shi dai Suleiman mai sana’ar Kalanzir ne a Kasuwar Kawo dake cikin garin Kaduna.

Bayan wata biyu da auran Suleiman da Amaryarsa Uwargidansa taki ta kwantar da hankalinta inda wata rana suna barci a daki, wato Mijin nata da sabuwar Amaryarsa sai uwargidan ta silalo dakin da suke barci ta watsa fetur a duk kusurwan dakin sannan ta fita t kulle su da kwano kafin ta kyasta ashana da ta ke rike da shi ta jefa a dakin.

Legit.ng ta samu labarin cewa wuta kuwa yace bani wuri ya kama ci bababababa. Da suka tashi suka nemi fita sai suka ji kofa a kulle. Nan ne fa suka fara yanka ihu har allah ya sa makwabta suka kawo musu dauki.

Sai dai kash abinka da wuta kafin hakan ya duk sun kusa konewa. Da aka balla kofar sai aka same duk a kwance da raunuka. Ba ayi wata wat aba sai aka kwashe su sai asibitin Barau Dikko dake Kaduna.

Wata mata ta kona mijinta da amaryarsa saboda bakin kishi a Arewa
Wata mata ta kona mijinta da amaryarsa saboda bakin kishi a Arewa
Asali: Twitter

Bayan kwana biyu sai rai yayi halinsa, wato Allah yayi wa Suleiman Kero, wato mijin rasuwa inda kuma ita Amaryar har yanzu tana asibti.

Bayan haka sai matar shi na farko wanda tana da yaya hudu duka mata ta dawo kwashe kayanta a boye domin ta gudu, makwabta kuwa suka yi ram da ita suka kuma mika ta ga ‘yan sanda.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel