Kalli ‘yar Najeriya da ta yi zarra a gasar musabakar al-Kur’ani ta duniya (HOTUNA)

Kalli ‘yar Najeriya da ta yi zarra a gasar musabakar al-Kur’ani ta duniya (HOTUNA)

- A'isha Musa Gale ta kasance zakarar gwajin dafi a gasar musabakar Kur'ani ta duniya da aka gudanar a kasar Malesiya

- A gasar masabukar Kur'ani da aka gudanar a baya, A'isha ce ta zo ta daya a bangaren mata, wanda hakan ya sa aka zabe ta a matsayin wadda za ta wakilci Najeriya

- Ta samu tarun kyaututtuka na alfarma

- Gwamnan jihar Bauchi Barista Muhammad Abdullahi Abubakar, ya jaddada mahimmancin ilimi ga al'umma

A'isha Musa Gale da ta fito daga karamar hukumar Alkaleri dake jihar Bauchi ta kasance zakarar gwajin dafi a gasar musabakar Kur'ani ta duniya da aka gudanar a kasar Malesiya.

Idan ba a mance ba a gasar masabukar Kur'ani ta kasa da aka gudanar a watannin baya, A'isha ce ta zo ta daya a bangaren mata, wanda hakan ya sa aka zabe ta a matsayin wadda za ta wakilci Najeriya a gasar ta duniya.

A yayin gasar musubakar ta duniya, A'isha ta samu kyautar gwal wanda kudinsa ya kai kimanin naira miliyan biyar, sannan kuma ta samu kudin da idan aka juya shi a kudin Najeriya ya kai kimanin naira miliyan biyu.

Kalli ‘yar Najeriya da ta yi zarra a gasar musabakar al-Kur’ani ta duniya (HOTO)
A'isha Musa a lokacin da gwamnan jihar Bauchi ke karrama ta

A yayi jawabin kwamitin musabakar ta duniya, sun jinjinawa gwamnatin Bauchi karkashin jagorancin Barista M.A Abubakar, wanda a cewar su muhimmancin da gwamnan ya baiwa harkar ilmi a jiharsa ne ya kai ga samun nasarar da yarinyar ta yi.

KU KARANTA KUMA: Mukaddashin Shugaban kasa Osinbajo na shirin karbo bashi

A jawabin sa ga kwamitin musabakar jihar Bauchi, Gwamna Barista Muhammad Abdullahi Abubakar, ya jaddada mahimmancin ilimi ga al'umma.

Legit.ng ta tattaro maku sauran hotunan jarumar a lokacin da ake karrama ta:

Kalli ‘yar Najeriya da ta yi zarra a gasar musabakar al-Kur’ani ta duniya (HOTO)
Kalli ‘yar Najeriya da ta yi zarra a gasar musabakar al-Kur’ani ta duniya
Kalli ‘yar Najeriya da ta yi zarra a gasar musabakar al-Kur’ani ta duniya (HOTO)
Aisha Musa 'yar jihar Bauchi da ta yi zarra a gasar musabakar al-Kur’ani ta duniya

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wa ya kamata a kama idan yaro ya saci jarrabawa? Malami, dalibi, ko kuma iyaye?

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng