Kungiyar Izala ta gina katafaren masaukin baki a Abuja (HOTUNA)
- Kungiyar Izala ta gina katafaren masaukin baki a babban birnin tarayya, Abuja
- Shugaban kungiyar Sheikh Bala Lau ne ya jagoranci gina masaukin a tsakiyar birnin tarayya
- An gina masaukin ne domin sauke bakin Allah 'Fi Sabilillah'
- An tara kudin gina gidan ne ta hanyar tattara fatun layya da Jama'a suka yi wanda bai yi na shekara biyu ba
Kungiyar Izala ta gina katafaren masaukin baki a babban birnin tarayyan Najeriya, Abuja.
Shugaban kungiyar ta Izala Sheikh Bala Lau neya jagoranci ginawa a tsakiyar birnin tarayya Abuja.
KU KARANTA KUMA: Kishin-kishin: Babachir ba zai dawo matsayin sa ba
An gina masaukin ne domin sauke bakin Allah a kyauta wato 'Fi Sabilillah'.
Legit.ng ta samu labarin cewa an tara kudin gina gidan ne ta hanyar tattara fatun layya da Jama'a suka yi wanda bai yi na shekara biyu ba.
Ga hotunan katafaren masaukin a kasa:
Shugaba Buhari ya bar Najeriya domin ganin Likita.
Asali: Legit.ng