Kaji abunda EFCC ta samu da ta kai farmaki gidan Kwankwaso?

Kaji abunda EFCC ta samu da ta kai farmaki gidan Kwankwaso?

- Hukumar EFCC ta kai samame gidan kanin tsohon Gwamnan jihar Kano kuma Sanata Rabiu Musa Kwankwaso bisa zargin an yi safarar motocin makamai da kudaden sata.

- A wata hira da BBC Hausa Kwankwaso ya ce EFCC sun balle garejin gidan kaninsa bisa zargin samun makamai da kudaden sata amma ga mamakin su sai ga Zomaye suna lamisar alaiyahu.

Legit.ng ta samu labarin cewa Kwankwaso ya bayyana farmakin a matsayin abin takaici kasancewar har ya gama gwamnati bai ja iyalai da ‘yan uwansa cikin gwamnati ba.

Kana kuma ya jagoranci kifar da gwamnatin Jonathan domin a samar da doka da tsari. A cewar sa da mai Malafa ne ya yi masa haka ba zai damu ba.

A wani labarin kuma, Majalisar dattawa ta ba da tabbacin zuwa makon gobe za ta kammala tantance kasafin kudin bana ta tura ga shugaba Muhammadu Buhari don sanya hannu.

Kaji abunda EFCC ta samu da ta kai farmaki gidan Kwankwaso?
Kaji abunda EFCC ta samu da ta kai farmaki gidan Kwankwaso?

KU KARANTA: Yadda za'a kwashe ta a 2019 - Elrufa'i

Mataimakin shugaban majalisar dattawan Ike Ikweremadu ya baiyana haka a lokacin da ya jagoranci zaman majalisar.

Ekweremadu ya bukaci ‘yan Nijeriya ka da su shiga zullumi kan kasafin kudin don shugaban kwamitin kasafi na majalisar dattawan Danjuma Goje da na majalisar wakilai na kammala aiki a matakin karshe don gabatarwa zauren majalisar kasafin don mika shi ga fadar shugaban kasa.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng