Karin albashi: A shirye nike in fara biyan ma'aikatan Gombe N56,000
- Gwamnatin jihar Gombe a karkashin jagorancin Gwamna Ibrahim Dankwambo ta ce a shirye take da ta soma biyan Naira dubu 56 a matsayin mafi karancin albahsin ma'aikata idan har gwamnatin tarayya ta amince da hakan.
- Gwamnan jihar shine ya sanar da hakan a ranar 1 ga watan Mayun da aka ware domin ma'aikata a duk fadin duniya.
Gwamnatin jihar Gombe a karkashin jagorancin Gwamna Ibrahim Dankwambo ta ce a shirye take da ta soma biyan Naira dubu 56 a matsayin mafi karancin albahsin ma'aikata idan har gwamnatin tarayya ta amince da hakan.
Gwamnan jihar shine ya sanar da hakan a ranar 1 ga watan Mayun da aka ware domin ma'aikata a duk fadin duniya.
Legit.ng ta tsinkayi Gwamnan ya kuma jaddada kudurin gwamnatin sa na wajen ganin tabbatar da jin dadin ma'aikatan jihar a kowanne fanni na rayuwa.
KU KARANTA: Abin da ya hana yi bayyana kaddara ta - Jonathan
Haka ma dai gwamnatin tarayya ta tabbar wa ma'aikatan kasar nan cewa ta shirya tsab domin sawa kudurin biyan karin mafi karancin albashi.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito, Shugaba Buhari ne ya bayyana haka a jawabinsa na ranar ma'aikata, gwamnati za ta duba batun kudurin gyaran albashi da wani kwamiti ya gabatar a ranar April 6, 2017.
Daga karshe kuma shugaban ya yi kira da kungiyar kwadagon da taimaka wa gwamnati wajen hada karfi da karfe domin domin tumbuke matsin tattalin arzikin da ya addabi Najeriya.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Bidiyon kungiyar kwadago a jiya
Asali: Legit.ng