Rashin lafiyar shugaba Buhari tayi kamari; ta kai ba ya iya cin abinci

Rashin lafiyar shugaba Buhari tayi kamari; ta kai ba ya iya cin abinci

– Rashin lafiyar shugaban kasa tayi kamari

– Abin kullum kara tabarbarewa yake yi

– Yanzu haka bai iya cin abinci ko ya sha ruwa

Yanzu haka rashin lafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari na kara tabarbarewa.

Jaridar Sahara Reporters ta fadi wannan labari.

Makonni fiye da uku kenan ba a ga shugaban kasar a taro ba.

Rashin lafiyar shugaba Buhari tayi kamari; ta kai ba ya iya cin abinci
Fadar shugaban kasa ta musanya labarin

Shugaban kasa Muhammadu Buhari bai halarci taron FEC da aka saba yi ba a wancan makon. Kusan dai makonni uku kenan ba a ga shugaba Buhari a taron Majalisar ba wanda ya ba Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo damar jan ragamar.

KU KARANTA: Babachir ya shiga cikin matsala

Rashin lafiyar shugaba Buhari tayi kamari; ta kai ba ya iya cin abinci
Lafiyar shugaba Buhari na tabarbarewa

Sahara Reporters tace kwana da kwanaki ke nan shugaban kasar yana fama da wahala wajen cin abinci ko shan wani abu. Hakan ta sa ko fita daga gidan sa ba zai iya ba. A Ranar Juma’a dai bai je masallaci ba.

Bayan dawowar shugaban kasar daga Landan abubuwa sun dan yi dama kafin kuma jikin ya kara kamari. Sai dai na-kusa da shi ba su da niyyar bari a kara fita da shi kasar waje domin a duba lafiya ta sa. Fadar shugaban kasa dai ta musanya wannan labari.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kana shan lemun Fanta ko su Sprite duk da illar su?

Asali: Legit.ng

Online view pixel