Kungiyar Izala ta gudanar da wa’azin ƙasa a garin Maiduguri (Hotuna)
- Malaman Izala sun gudanar da wa'azin kasa a garin Maiduguri
- Taron wa'zin ya samu halartan dimbin jama'a
Kungiyar Jama’atil Izalatil Bidi’a wa Iqamatissunnah ta kasa, JIBWIS, ta gudanar da wa’azin kasa a tsakiyar garin Maiduguri, na jihar Borno.
Abin dadin shine taron wa’azin kasan ya gudana lafiya cikin kwanciyar hankali ba tare da wani fargaba ba, ko makamancin hakan, kamar yadda jaridar Rariya ta ruwaito.
KU KARANTA: Jaki ya zama gwal a Jigawa, nemansa ake ruwa a jallo, kasan dalili?
Bugu da kari, dubunnan jama’a ne suka yi dafifi suka halarci taron wa’azin na bana, wanda hakan ke alamta cewar kwanciyar hankali da zaman lafiya ya soma dawowa jihar Borno, wanda a baya tayi fama da matsalolin hare haren ta’addanci na Boko Haram.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito manyan malamai da suka hada da shugaban kungiyar, Sheikh Abdullahi Bala Lau, da shahararren maja baki Ahmad Sulaiman sun samu halartan taron. An hangi keyar Sheikh Giro Argungu a yayin taron da sauran manyan malamai.
Tun a shekarar 2009 ne dai aka fara rikicin Boko Haram wanda yayi sanadiyyar mutuwar dubunnan jama’a a jihar Borno tare da mayar da miliyoyin mutane yan gudun Hijira.
Ga sauran hotunan nan:
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Kalli barnar da Boko Haram tayi a Borno
Asali: Legit.ng