Madalla! Yan sanda sun kama wani kato lokacin da ake badala da wani yaro
- Jami'an hukumar 'yan sanda na karamar hukumar Kontagora dake jihar Neja sun sake cika hannu da wani magidanci
- Magidancin sunan sa Awwal Abdullahi dake zaune a unguwar Dadinkowa
- An kama shi ne bisa zarginsa da aikata laifin luwadi da wani yaro dan kimanin shekara 12.
Jami'an sun samu nasarar kamashine ta hanyar rahoton da mazauna unguwar suka basu na zargin sa da lalata masu yara ta hanyar luwadi, nan take 'yan sandan suka hada kai da jami'an Hisba wadanda suka cigaba da sa ido akansa har Allah yabasu nasarar kamashi alokacin da yake luwadi da yaron a jiya litinin.
Legit.ng ta samu labarin cewa wanda ake zargin ya amsa laifin yayi luwadi da wannan yaron sau biyu, saidai ya baiyana cewar bisa kaddara ne domin ba aikinsa bane,
Mazauna unguwar sun tabbatar da cewar wannan bashine karonsa na farko ba domin sun sha ganinsa yana shiga da kanan yara a gidan sa, aduk lokacin da zai aikata luwadi da yaran sai ya tura matarsa unguwa ko ya dauki yaron zuwa wani unguwa,-inji su.
KU KARANTA: Jami'an tsaro sunyi wa dalibai rubdugu a Kogi
Wannan dai bashine karon farko da hakan ke faruwa a garin Kontagora ba, domin a makonnin baya ansamu laifin aikata luwadi da fyade kimanin guda 5 daya daga ciki shine na Maishayin da yayima wani yaro mai suna Aminu luwadi wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar yaron.
Saidai shugaban karamar hukumar Kontagora Alhaji Ahmad Attahir (Baban-makaranta) yasha alwashin tabbatar da an hukunta duk wanda akasamu da laifin aikata luwadi ko fyade da yara a garin, yakumayi kira ga al'umma da sucigaba da baiyana duk wanda suka san yana aikata wannan mummunar dabi'a,
Jami'an 'yan sanda na A'dibishon kontagora na cigaba da tsare wanda ake zargin (Awwal Abdullahi) domin cigaba da gudanar da bincike inda suka baiyana cewar a karshe za su gabatar da shi gaban kotu domin ya fuskanci hukunci.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Nan ma dai wani kato ne dake aikin daga nauyi
Asali: Legit.ng