An sulhunta rikicin dake tsakanin Nafisa Abdullahi da Hadiza Gabon (Hotuna)
- An shawo kan rikicin da ya shiga tsakanin Nafisa Abdullahi da Hadiza Gabon
- Rikicin nasu ya faro ne tun a jihar Kaduna yayin da suke dandalin shirya fina finai
A jiya Alhamis 20 ga watan Afrilu ne kungiyar mashirya fina finai na Kannywood suka shiga tsakanin jaruman yan fim din nan su biyu Nafisa Abdullahi da Hadiza Gabon bayan wata arkalla data shiga tsakaninsu.
Shaidan dai ya shiga tsakanin jarumai matan ne a jihar Kaduna yayin da suke bakin aiki wajen shirya wani fim a garin na Kaduna, kamar yadda jaridar Rariya ta ruwaito.
KU KARANTA: Rikita-Rikita: Rahma Sadau ta maka Nafisa Abdullahi kotu (Dalili)
Sai dai kungiyar mashirya finafinan Kannywood, MOPPAN tace ba zata zura idanu yayanta suna fada da juna ba, hakan ta sanya su shiga tsakanin sulhunta su. Daga karshe an hangi jaruman biyu suna murmushi tare da rungumar juna.
Wasu daga cikin wadandu suka halarci zaman sulhun sun hada da Hajara Daso, Kabiru Maikaba, Nafisa Abdullahi, Hadiza Gabon da sauran manyan kungiyar.asu daga cikin wadandu suka halarci zaman sulhun sun hada da Hajara Daso, Kabiru Maikaba, Nafisa Abdullahi, Hadiza Gabon da sauran manyan kungiyar.
Wasu daga cikin wadandu suka halarci zaman sulhun sun hada da Hajara Daso, Kabiru Maikaba, Nafisa Abdullahi, Hadiza Gabon da sauran manyan kungiyar.
A wani labarin fitacciyar jarumar nan Rahama Sadau kuma ta maka Nafisa Abdullahi gaban kotun Nomans land dake jihar Kano. Dalilin wannan katankatana kuma shine Rahama tayi zargin Nafisa bata biya ta kudin data ranta mata bane.
A wani labarin fitacciyar jarumar nan Rahama Sadau kuma ta maka Nafisa Abdullahi gaban kotun Nomans land dake jihar Kano. Dalilin wannan katankatana kuma shine Rahama tayi zargin Nafisa bata biya ta kudin data ranta mata bane.
S
ai dai Nafisa Abdullahi ta musanta zargin, inda tace “Ni ba wasu kudi da Rahma ta bani dan nayi mata fim. Abinda nasani shine, tace tanaso na fito acikin fim din ta maisuna RARIYA nace zan fito amma sabida wasu dalilai ban fito ba, amma ni ba wasu kudi da ta bani.”
Majiyar Legit.ng ta ruwaito za'aci gaba da sauraron shari'ar ranar litinin 24 ga watan Afrilu.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Yadda Yarbawa suka ceci Hausawa a rikcin Ife
Asali: Legit.ng