Jihohi 12 da za su koma Biyafara idan an raba Najeriya

Jihohi 12 da za su koma Biyafara idan an raba Najeriya

– Har yanzu wasu na kokarin ganin an raba kasar nan

– Wasu na neman kasar Biyafara mai zaman kan-ta

– A dalilin haka ne aka gwabza yakin basasa

Jihohi 12 da za su koma Biyafara idan an raba Najeriya
Masu neman Kasar Biyafara daga Najeriya

Kawo yanzu haka wasu ‘Yan can kudancin kasar na kokarin ganin an raba Najeriya su balle zuwa Yankin Biyafara a matsayin kasa mai zaman kan ta. A dalilin haka ne ma aka gwabza yakin basasa shekaru 50 da suka wuce.

Idan dai har an raba kasar wanda zai yi wahala kamar yadda wani masanin tsarin mulki Farfesa Auwal Yadudu ya fada kwanan nan, akwai Jihohin da za su bar Najeriya su koma Kasar Biyafara. Ga su nan Legit.ng sun kawo su a jere:

KU KARANTA: Rikicin Kudancin Kaduna; Buratai ya kai ziyara

Jihohi 12 da za su koma Biyafara idan an raba Najeriya
Tutar Biyafara idan an raba Najeriya

1. Abia

2. Anambra

3. Akwa-Ibom

4. Bayelsa

5. Cross-River

6. Ebonyi

7. Enugu

8. Imo

9. Delta

10. Rivers

11. Bangaren Edo

12. Bangaren Benue

Kwanaki tsohon shugaban kasa wanda yayi mulki a lokacin yakin Janar Yakubu Gowon ya bayyana yadda ya hana Najeriya wargajewa. Gowon ya bayyana haka ne a Ranar tunawa da Marigayi Awolowo sai dai yanzu yace Najeriya na bukatar addu’a.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani babban Fasto ya musulunta a Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel