Har yau na fi ‘Yan matan fim aji – Ummi ZeeZee

Har yau na fi ‘Yan matan fim aji – Ummi ZeeZee

- Ummi Ibrahim ZeeZee ta kasance shahararriyar ‘yar fim ce wacce ta ci zamanin ta a baya

- Jarumar ta bayyana cewa ita ta fi ‘yan fim aji

- Ta kuma jadadda soyayyarta da tsohon shugaban kasa Ibrahim Babangida

Ummi Ibrahim ZeeZee ta kasance shahararriyar ‘yar fim ce wacce ta ci zamanin ta tsakanin 2004 zuwa 2006.

A cikin wata hira da akayi da jarumar, ta bayyana cewa tafi yan fim aji, domin ita asali a kasar Saudiyya take zaune. Asali ma ta shiga harkan fim ne kawai don sha’awa da ra’ayi amma ba wai domin kudin da za’a biya ta ba.

Da aka tambayi jarumar kan cewa ko ta taba yin furucin cewa ta fi yan fim aji, Jarumar tace: “Wannan ma ai ba sai ka tambaya ba. Ka tuna fa ni da farko a Saudiyya ma na ke zaune. Amma da na yi wani zuwa Nijeriya, sai na yi sha’awar harkar fim. To tun cikin 2004 ban sake zama Saudiyya ba, sai dai na je aikin Hajji ko Umra na dawo. Ni fa har yau ban taba fashin zuwa Umra ba. Kuma aikin Hajji na sha yi ba sau daya ko sau biyu ba.”

Har yau na fi ‘Yan matan fim aji – Ummi ZeeZee
Tsohuwar yar wasan Kannywood, Ummi Ibrahim ZeeZee

“Ko a lokacin da na ke yin fim, ni ba don neman kudi na ke yi ba. Kawai sha’awa ce. Kusan kashi 95% bisa 100% idan na yi fim ba na ma karbar ladar da za a biya ni. Su kan su furodusoshin ma sun sani, ko sun ba ni wani lokaci a wurin zan rabar da kudin, ko kuma idan na je gida na ba mabukata."

KU KARANTA KUMA: Kalli kywawan hotunan sabuwar matar Ahmed Musa guda 8

Ku tuna a baya Legit.ng ta kawo labarin jita-jitan soyayya a tsakanin jarumar da tsohon shugaban kasa, Ibrahim Babangida.

Da aka zo kan al’amarin soyayyar ta da tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Babangida ta ce: “To ni dai tun ina sakandare IBB shi ne gwarzo kuma gwani na a duk cikin shugabannin kasar nan da aka yi. To daga baya muka hadu, kuma da aure na ke son sa.

“Idan babu soyayya a tsakanin mu zan fito na ce akwai ne? Ya taba cewa karya na ke yi? Ko ya taba cewa na daina fada?

“Babban mutum kamar IBB na isa na fito na yi masa karya ne? Idan bai san da maganar ba, ai sai ya fito ya ce karya na ke yi.

Shi ya sa wai idan ka ji an ce wai na ce a kasuwa na ke ko kaza da kaza, to ni ba a kasuwa na ke ba. Na fi karfin na yi tallar kai na. Aji na ya wuce na tallata kai na. Roko na a yi mana addu’ar fatan alheri kawai.”

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

An ba dan gasar BBNaija da yayi nasara Naira miliyan 25 da SUV:

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel