Dalilai 3 da za su mu godewa Aliko Dangote
– Alhaji Aliko Dangote mai kudin Afrika ya cika shekara 60 a Duniya
– Dangote yana cikin mutane 100 masu kudin Duniya
– Jama’a na samun alheri daga dukiyar Dangote
Kwanan nan ne Attajirin Duniyar nan watau Alhaji Aliko Dangote ya cika shekaru 60 da haihuwa. Har shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika takarda ga babban dan kasuwa domin taya sa murna, shugaba Buhari yace Dangote ba ya nuna bambanci wajen tafiya da kowa. Akwai dai dalilai da dama da za su sa dole a godewa Allah da ya ba Dangote arziki.
1. Kamfanin tatar mai
Idan har aka kammala aikin masana’antar tatar man Dangote wanda duk Duniya babu irin sa, Najeriya ta huta da wahalar fetur da sauran su irin takin zamani. Har dai Najeriya za ta rika samun kudin shiga na Dala.
KU KARANTA: Farashin shinkafa zai fadi kasa
2. Kayan gini watau Siminti
Ba Najeriya kadai ba kusan mafi yawan kasashen Afrika Aliko Dangote ya shiga ya bude kamfanin siminti domin masu gini. Wannan dai ya taimakawa magina a fadin Nahiyar da siminti na cikin gida.
3. Abinci
Alhaji Dangote ya samawa Jama’a da dama aiki wanda bayan Gwamnatin tarayya babu mai yawan ma’aikatan sa. Dangote dai yana da kamfunan kayan abinci irin su taliya da sauran su a Najeriya.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Mai ya kawo tashin farashin kaya a kasuwa?
Asali: Legit.ng