Manyan kalamai 13 daga sabon bidiyon da Boko Haram ta saki
Kungiyar ta’addan Boko Haram ta fitar da wani sabon bidiyo wanda aci tayi wasu kalamai da dama ciki harda kalubalantar shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari da kuma kundin tsarin mulkin kasar, harma da al’umman Najeriya baki daya.
Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin manyan kalamai da kungiyar ta Boko Haram tayi a cikin bidiyon.
KU KARANTA KUMA: Labari da Dumi-Dumi: Boko Haram su yi wani sabon bidiyoLabari da Dumi-Dumi: Boko Haram su yi wani sabon bidiyo
Ga yadda kalaman suka zo kamar haka:
1. Al-Qur’ani muke dauka bazamu bi kundin tsarin mulki ba (constitution). Litaffin da ake bi yahudu da nasara ne suka rubuta shi suka sanya masa suna constitution.
2. Sun kuma cire tutar la’ilaha ilallahu suka kawo mana wata shgiyar tuta wanda kashi ya fita daraja itace kore fari kore (green white green) suka basa,
3. Mallam Muhammad yusuf yace tunda wannan ba littafin mu bane ‘constitution’ mu kyale shi . Kore fari kore na Najeriya ba tutar annabi bane mu kyale shi muzo mu kafa Qur’ani da Hadisi, muzo mu kafa tutar lah ilaha ilallahu a Najeriya gaba dayan mu muzo mu bi hukuncin Qur’ani.
4. Yace karda mu bauta wa kasa saidai mu bauta wa Allah shi kadai
5. Kowa ya yarda da cewan wa’azin mallam yusuf gaskiya ne ko mallaman izala sun yarda. A karshe suka ki gaskiyan suka kashe mana imamun mu na farko kuma jinin mallam yusuf yana da tsada a wajen mu yafi jinin mutanen najeriya gaba daya
6. Gwanda ace babu mutanen Najeriya gaba daya daga Buhari, ministoci, gwamnoni alkalan sa, sojojin sa ma’aikatan sa yafi mana sauki a kan jinin mallam yusuf
7. An zub da jininsa amma Allah ya kafa mana daular musulunci
8. Muna cikin daular musulunci muna cikin koshin lafiya babu wani abinci da muka raa a wannan dajin sambisan.
9. Duk wanda yace Boko Haram sun rasa karfin su sun rasa abinci to wallahi karyane.
10. Muna cikin koshin lafiya ga ma’aikatan mu baki daya muna nan ku duba jikinmu anan zaku tabbatar da cewa muna nan cikin lafiya. Duk abunda yan Nanjeriya suke ci muma muna ci.
11. Allah ya sake daura mana limami na biyu gwarzo wanda shine dodon yahudawa kuma ya kasance makokwaron najeriya wato abubakar shekau. Allah ya bar mana limamin mu, Allah yasa muyi masa biyayya dari bisa dari.
12. Limaminmu abubakar shekau na nan lafiyar sa kalau, karyane babu wanda ya kashe shi, Abubakar shekau ne shugaban najeriya a wajen mu
13. Bamu san wani shugaban kasa wai Buhari ba, shugaban yahudu da nasara ne, shugaban kafirci ne, Buhari shugaban kiristoci ne, Buhari ba shugaban musulunci ba.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Kalli bidiyon a kasa:
Asali: Legit.ng