Dandalin Kannywood: Nafisa Abdullahi ta fito da 'aski' a sabom fim din Sultana

Dandalin Kannywood: Nafisa Abdullahi ta fito da 'aski' a sabom fim din Sultana

Jaruma Nafisa Abdullahi tana daga jerin jaruman da babu kamarta awajen iya acting a film. sabida gogewarta ne yasa ta dauki gwarzuwar shekara yafi sau uku tun farkon fara fim din ta kawo yanzu.

Nafisa Abdullahi ta fito da 'aski' a sabom fim din Sultana
Nafisa Abdullahi ta fito da 'aski' a sabom fim din Sultana

Yanzu ta kuma fitowa a wani babban fim na mawaki Nura M Inuwa, sunan fim din ' SULTANA'. wanda jaruma Nafisa ta fito awani matsayi daba kasafai akacika ganin mata sun fito ba. Domin anyiwa Nafisa Abdullahi Kwal da Kwabo. An aske gashin kanta gaba daya. Wanda haka ya yi sanadiyyar canja mata siffa, siffarta ta koma irin siffar Namijin Saurayi.

KU KARANTA: Majalisar kano ta yanke dokar karshe kan hana aure

Legit.ng ta samu labarin cewa anyi tsada da Nafisa akan za'a bata naira milliyan daya da dubu dari daya 1.1 million. Da farko Halima Atete akaso ta fito a fim din amma tace ita gaskiya ba zata iya ba. Sabida ba zata yarda ayi mata aski ba. Haka kuma ace jaruma Fati Washa ta fito acikin fim din Sultana amma tace ba zata iya ba. Wanda na ukune aka sami Nafisa Abdullahi tace zata iya fitowa amatsatin jarumar fim din 'SULTANA.

Wannan karfin hali da bajinta da Nafisa Abdullahi ta nuna yasa manyan jarumai ciki harda Adam A Zango suka jinjinawa jaruma Nafisa Abdullahi akan wannan namijin kokari da tayi.

Dama Jaruma idan ta cika jaruma shine ta fitowa ako wanne matsayi da aka sa ta tafito. Dan haka dole a jinjinawa Nafisa Abdullahi domin ta cika jaruma.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan ma wani jarumi ne ke bayanin yadda matar sa ta sa boye yana da aure

Asali: Legit.ng

Online view pixel