Abin da ya sa na auri mata 2 a rana guda Inji wani Dan Neja-Delta

Abin da ya sa na auri mata 2 a rana guda Inji wani Dan Neja-Delta

Wani Ta’aliki ya auri mata har 2 kuma a rana guda kwanan a Jihar Deltan Najeriya. Wannan abu dai ba a saba jin sa ba musamman a irin wannan yanki na kudancin kasar

Abin da ya sa na auri mata 2 a rana guda Inji wani Dan Neja-Delta
Bikin aure a Yankin Neja-Delta

Omamuzo Utomajiri wani mutumin Neja-Delta ne yayi wani abin da ba a saba gani ko ji a Yankin Neja-Delta ba inda ya hada mata 2 ya aure a rana guda abin sa. Utomajiri ya bayyana dalilin sa na yin hakan.

Wannan Bawan Allah kuma dan kasuwa da ke Uro-Irri na karamar hukumar Isoko kamar yadda Legit.ng ke samun labari yace ya auro mata 2 ne domin ya zama babu ruwan sa da wasu mata a waje.

KU KARANTA: Ya za a kare?: Batun dokar aure a Kano

Shi dai wannan mutumi yana sana’ar saida katako ne da kayan gini wanda kuma kowace mata ke kula da na ta barayin Inji wannan Angon na mata biyu. An dai daura auren ne a Ranar 26 ga watan Maris dinnan yace kuma suna son junan su.

Haka kuma a can kasar gabas wani kare yayi sanadiyar cecen rayuwar mutane masu dinbin yawa a Garin Borno inda ya hana wata yarinya tada bam a wani gidan biki

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Mace mai kamar maza; ka ga Makaniki mace a bakin aiki

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel