Real Madrid da Barcelona sun kafa tarihi

Real Madrid da Barcelona sun kafa tarihi

– Neymar Jr. ya ci kwallon sa ta 100 a Barcelona

– Shekarar Neymar kusan 4 a Kungiyar Barcelona

– Haka ma Real Madrid ba a bar ta a baya ba

Real Madrid da Barcelona sun kafa tarihi
Neymar ya shiga tarihin Barcelona

Dan wasan gaban nan na Barcelona watau Neymar Jr. ya jefa kwallon sa na 100 a zaman sa a Barcelona jiya a wani wasa da su ka buga. Barcelona dai ta lallasa Kungiyar Granada da ci 4- 1 a wasan na La-liga.

Kamar yadda Legit.ng ke samun rahoto dai hakan na nuna cewa da wuya dan wasa Neymar ya bar Barcelona bayan da ya ci kwallon san a 100 a cikin wasanni 177 rak bayan zuwan sa Kungiyar a 2013.

KU KARANTA: An daure wani Malami a Jihar kano

Real Madrid da Barcelona sun kafa tarihi
Kungiyar Real Madrid ta kafa tarihi a Spain

Haka kuma Real Madrid ta lallasa takwarar ta Alaves da ci 4-0 watau har da nema. Kusan dai Barcelona da sauran manyan Kungiyoyin kasar Spain sun gaza cin kungiyar Alaves a gida. Wasanni sama da 50 kenan a jere kullum sai Real Madrid ta jefa kwallo a raga.

Ku na da labari cewa FIFA ta Duniya ta dakatar da babban dan wasan nan na kasar Argentina Lionel Messi da ke Barcelona. Dan wasan gaban ba zai buga wasanni 4 ba bayan an same sa da laifin fadawa Alkalin wasa maganganun da ba su dace ba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko http://twitter.com/naijcomhausa

Ka taba ganun makanike mace kuwa?

Asali: Legit.ng

Online view pixel