Sanata Ibn Na’Allah ya sha da kyar a garin Zuru

Sanata Ibn Na’Allah ya sha da kyar a garin Zuru

Sanata Bala Ibn Na'Allah ya sha da kyar, inda mafusatan da suka halarci wurin bada tallafin suka yi ta ihun ba sa so a karamar hukumar Zuru dake jihar Kebbi.

Sanata Ibn Na’Allah ya sha da kyar a garin Zuru
Sanata Bala Ibn Na’Allah

A yayin da Sanata Bala Ibn Na'Allah ya je raba injina da babura a garin Zuru dake jihar Kebbi a yammacin yau Lahadi, rahotanni sun nuna cewa ya sha da kyar, inda mafusatan da suka halarci wurin bada tallafin suka yi ta ihun ba sa so, saboda adawar da ke tsakanin 'yan majalisar dattijan da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya yanke hukuncin karshe a kan Magu yayinda ya yi zaman lafiya da majalisa

Legit.ng ta samu labarin cewa daga bisani jami'an tsaro sun dauke Sanatan daga wajen, daga bisani kuma aka karo jami'an tsaro, inda bayan zuwan su suka soma kama wasu daga cikin matasan dake zanga-zangar.

Bayan jami'an tsaro sun kama jama'a a wurin taron, dandazon jama'a sun yi dafifi a kofar ofishin 'yan inda suka yi ikrarin cewa babu wanda ya isa ya sa a rufe matsan, inda daga baya wani na kusa da Sanatan ya zo wajen ya umarci jami'an 'yan sandan da su saki wadandan aka kama.

Wani mutumi ya bayyana danasanin zaben jam'iyyar APC

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng