An kama masu kai wa daliban Najeriya hari a India
Jami’an ‘yan sandan India sun cafke mutane shida da ake zargi da hannu wajen kaddamar da farmaki kan daliban Najeriya da ke karatu a kasar, abin da masu rajin kare hakkin dan adam suka bayyana a matsayin laifin nuna kyama.
Legit.ng dai ta gano wasu hotuna da aka watsa a kafafen sada zumunta sun nuna yadda wasu matasan India ke amfani da sandina da kujerun karfe wajen dukan daliban Najeriya a Greater Noida.
Wani babban Jami’an ‘yan sandan kasar Sujata Singh ya shaida wa majiyar mu cewa, nan gaba za su sake kama wasu mutane hudu da ake zargi a wannan lamari da ya dauki hankulan ‘yan Najeriya.
KU KARANTA: Hukumar WAEC ta fallasa wani Sanata
Hukumomin Najeriya sun kira jakadan India a kasar don amsa tambayoyi a birnin Abuja kan wannan batu.
An dai kai wa ‘yan Najeriyar hari ne bayan mutuwar wani dan India sakamakon kwan-kwadon kwayoyi fiye da kima, amma mazauna yankin Greater Nida suka zargi ‘yan Najeriya da hannu a mutuwarsa.
Kazalika farmakin ya shafi sauran daliban nahiyar Afrika da ke karatu a kasar ta India, lamarin da ya sa jami’an tsaro ke yi musu rakiya zuwa makarantu da shaguna don kare lafiyarsu.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Ga kuma wata uwa nan tana kuka an tafi mata da yaya
Asali: Legit.ng